<
Notice
Barka da zuwa Hujjah.Com.ng. Sanarwa, Wannan shafin An Gina Shine Domin Al'ummar Hausawa Gabadaya, Saboda Haka Kowa Ze Iya Regista Kuma Yayi Posting Acikin Shafin. Zaku iya tuntubar admin Contact Admin ko Facebook Page domin Aiko Mana Da Sakonninku, Mungode. info@hujjah.com.ng
HomeYoutube[YouTube Upload] Yadda Ake Dora Video a YouTube

Posted by , May 8, 2019

Posted Under: Youtube, 47 Views

[YouTube] Yadda Ake Dora Video a YouTube

Menene YouTube:

YouTube daya ne daga cikin shafukan sadarwa na yanar gizo mallakar kamfanin Google wanda ke baiwa mutum damar kallar video da kuma dora video a kai, ta yadda zai samu damar aikawa da mutane sakon video,

YouTube shine shafi na biyu a duniya da al’umma suka fi ziyarta.

adireshin YouTube shine www.youtube.com

Yadda ake dora Video a YouTube:

Yadda ake dora video a YouTube shine a computer zaka ga alamar “Upload” da zarar ka shiga YouTube ko kuma kai tsaye kaje www.youtube.com/upload
Hujjah.Com.ng
A waya kuma akwai shima ta sa alamar ta uploading kamar yadda kuke gani a kasa.

PopAds.net - The Best Popunder Adnetwork

Hujjah.Com.ng
Hujjah.Com.ng

Kana shiga zai budo maka dukkan videos din dake kan wayarka sai ka zabi wanda kake son uploading, idan kuma live zakayi akwai alamar “Go” a wajen.

READ>>  [Karanta Yanzu] Yadda zaka samu Subscribers a YouTube Channel dinka

Abubuwan da Zaka Kula Dasu Wajen Yin Uploading

1. Title
2. Description
3. Tag
4. Featured Image
5. Privacy

Title: a nan zaka saka taken (sunan) Videonka ana buka
Tar ka sanya take mai jan hankali sosai.

Reliable Web Hosting in Nigeria by DomainKing.NG

Description: a nan zaka tsara takaitaccen bayani akan abinda videonka ya kunsa. (amman a waya a nan ake saka tag).

Tag: shine ka sanya kalmomin da kake ganin za’a iya yin searching ko kake son suga videonka, akwai cikakken bayani ka nemi darasinmu na HashTag.

READ>>  Yadda Zaka Samu Kudi Ta YouTube 002

Featured Image: Shine hoton da kake so ka gani akan videon, misali zaka ga a YouTube ance “Ka San Abin Kunyar Da Maryam Yahaya Tayi? Ga hotonta kuma akai, amman kana shiga sai ka ga ba Maryam Yahaya bace. To a nan ne ake saka irin wannan hoton. (amman yin wancan salon kuma yaudara ce ya sabawa addininmu).

Privacy: shine yadda zaka zabi suwa kake so su kalli videon ka.

YouTube Privacy:

YouTube Privacy shine a wajen dora videonka zaka zabi suwa kake so su ga videon ka? Privacy a YouTube ya rabu gida uku (3) kamar haka:

1. Private
2. Unlisted
3. Published

Private: shine babu wanda zai ga videon sai kai kadai.

READ>>  [Youtube] Yadda Ake Samun Kudi Ta YouTube:

Unlisted: shine baka son kowa ya ga videon sai wanda ka turawa link dinsa. (shine ga masu sayar da video a YouTube).

Published: shine ka sanya videonka yadda kowa da kowa zai iya gani.
Zan dakata a nan sai a rubutu na gaba.

Posted By: Basheer Sharfadi
E-mail info@hujjah.com.ng

About Author (107)

Administrator

Sunana: Sulaiman Aliyu Yahaya , Wanda Akafi Sani Da [Ibn Hujjah] Ni Haifaffen Garin Kano Ne, Nayi Karatuna Na Primary , A Nan Sheka Kumbotso L.G Nayi Secondry A G.S.S Shekar Barde, Nagama Karatuna Na Secondry, A Shekarar 2017, Yanzu Haka Ina Karatuna Akan Computer. Zaku Iya Kirana Ta No: 08163286393

Leave a Reply
Email Subscription
Saka email dinka kayi subsciption domin samun sabbin darussa a email dinka
Contact Us

Contact Us