<
Notice
Barka da zuwa Hujjah.Com.ng. Sanarwa, Wannan shafin An Gina Shine Domin Al'ummar Hausawa Gabadaya, Saboda Haka Kowa Ze Iya Regista Kuma Yayi Posting Acikin Shafin. Zaku iya tuntubar admin Contact Admin ko Facebook Page domin Aiko Mana Da Sakonninku, Mungode. info@hujjah.com.ng
HomeSocial Media[WhatsApp] Dalilan da Suke Saka WhatsApp Ke Dakatar da Mutum daga WhatsApp

Posted by , March 9, 2019

Posted Under: Social Media, 102 Views

[WhatsApp] Dalilan da Yasa WhatsApp Ke Dakatar da Mutum daga WhatsApp

A kwanakin nan na samu korafe-korafe da dama daga ‘yan uwa kan dandalin sada zumunya na WhatsApp sunyi Banning nasu wato sun rufe lambar mutum bashi da damar yin WhatsApp, kana kai zasu koreka kamar dai yadda Facebook keyin Blocking

Wannan sabon abune ga wasu, amman dama can akwai wannan tsarin sai dai kawai yanzu za’a iya cewa irin ta shugaban Nigeria da yace da zafi-zafi za’ayi Next Level, to suma sun gwadata ne a nan wajen daukan mataki mai tsauri.

Kar na cikaku da surutu ina tafe da dalilan dake sawa WhastApp su sallami mutum don haka sai kayi kokarin kiyayewa gudun samun matsala, kana ji kana gani duk dadin WhatsApp dinnan ace sai ka canja lamba.

1. Yin amfani da wani Application a madadin WhastApp ko mai taimaka masa, akwai WhatsApp kala-kala amman guda daya tak wanda kuke gani a Play Store shi kadaine mallakar kamfanin WhatsApp kuma bayaso kayi amfani da wanda ba nasa ba, amman zaka ga Apps sunyi kare-kare sosai abubuwan da baka iya yi a WhatsApp su zaka iya yi a kansu, to WhatsApp baya son wannan kuma yana rufe lambar duk masu yin amfani da irin wadannan Application.

PopAds.net - The Best Popunder Adnetwork

2. Yawan tura sako ga wanda bashi da lambarka, takurawace mutum bashi dalambar ka, ka dameshi da tura masa sako, WhatsApp sun dauki wannan a matsayin laifi domin kana musgunawa wani, don haka tilas mutum ya guji yawan tura sako ga lambar da mai lambar bashi da taka lambar, matukar kana yawan yin hakan to zasu rufe lambarka, duk wanda zakuyi chat kayi masa Hands-free kace masa yayi saving lambarka.

READ>>  [Instagram] Yadda Zakayi Posting a Account sama da guda daya a lokaci Guda

3. Ka dinga saka mutane a Group wadanda basu da lambarka, haka kawai sai mutum ya bude Group baka da lambarsa kaga ya saka ka aciki ka fita ya kara adding dinka, wannan shima babban laifine a kundin WhatsApp yana da kyau duk wanda zaka saka a Group ya zama yana da lambarka kaima kana da tasa, wannan shine ya sanya da yawa aka dinga rufe lambobin masu Group saboda kawai zasuce duk me son shiga group ya basu lambarsa, a maimakon hakan gwara ka fitar da link na Group.

READ>>  [Cigaba] An Fara Dora Audio A Instagram

4. Idan ka aikata daya daga cikin wadancan laifukan sai mutane suka dinga yin reporting dinka to shima WhatsApp zai kori lambarka, misali ka sakani a Groupn a fita ka kuma sani to a karo na biyu zan fara Blocking dinka ne sannan na fita, to WhatsApp suna lura da wannnan.

READ>>  [Instagram] Tsarin Tallata Kasuwanci ta Shafin Instagram

Daya daga cikin wannan dalilan shi zaisa kana cikin WhatsApp sai kaga an koroka waje an rubuta maka Your phone number ******** is temporarily banned from WhatsApp. Contact Support

Reliable Web Hosting in Nigeria by DomainKing.NG

Wato dai an rufe Account dinka na WhatsApp.

Zan dakata a nan sai a rubutu na gaba.

Posted by: Basheer Sharfadi
Email: info@hujjah.com.ng

About Author (107)

Administrator

Sunana: Sulaiman Aliyu Yahaya , Wanda Akafi Sani Da [Ibn Hujjah] Ni Haifaffen Garin Kano Ne, Nayi Karatuna Na Primary , A Nan Sheka Kumbotso L.G Nayi Secondry A G.S.S Shekar Barde, Nagama Karatuna Na Secondry, A Shekarar 2017, Yanzu Haka Ina Karatuna Akan Computer. Zaku Iya Kirana Ta No: 08163286393

Leave a Reply
Email Subscription
Saka email dinka kayi subsciption domin samun sabbin darussa a email dinka
Contact Us

Contact Us