<
Notice
Barka da zuwa Hujjah.Com.ng. Sanarwa, Wannan shafin An Gina Shine Domin Al'ummar Hausawa Gabadaya, Saboda Haka Kowa Ze Iya Regista Kuma Yayi Posting Acikin Shafin. Zaku iya tuntubar admin Contact Admin ko Facebook Page domin Aiko Mana Da Sakonninku, Mungode. info@hujjah.com.ng
HomeMarketing, Online Money, Social Media[Online Business] Abubuwa Guda (20) Da Zasu Taimaka Maka Wajen Bunkasa Kasuwancinka Ta Social Media

Posted by , April 4, 2019

Posted Under: Marketing, Online Money, Social Media, 129 Views

Kana son sanin yadda zaka bunkasa kasuwancinka karami ko babba ta Social Media cikin ‘yan watanni masu zuwa?

Kana son sanin irin ribar da kasuwancin yanar gizo keda shi?

A yau ina tafe da bayanin wasu muhimman abubuwa wanda mutum zai rika matsayin wukar kugu domin ya bunkasa kasuwancinsa ta shafukan sada zumunta da muke amfani dasu.

Eh! Shafukan sada zumunta dai su Facebook, Instagram, da WhatsApp da muke amfani dasu, kada na cikaku da surutu ku biyoni kawai.

1. Social Media zai hada ka da jama’a wadanda basu sanka ba, baku ma su san sana’arka ba, da kuma wanda sun sanka amman basu san sana’arka ba don haka ko suna da bukata zasu wuce ka. Kayi tunani shin Social Media ta taba hadaka da mutane?

Ka duba Instagram mafi yawan mutane zasu ce sunga kaya masu kyau a Insta.

2. Bayan Social Media ya hadaka da mutane kuma zai sanya su sayi kayanka, Ba ruwan social media da abinda kake siyarwa kawai shi zai baka dama don ka tallatawa jama’a kayanka shi kuma ya hadaka da masu siya.

3. Ka dinga bibiyar social media akai-akai, wani zaka ga yana shiga social media sau daya a rana sau daya, to amman ga wanda ke son bunkasa kasuwancinsa dole ya dinga shiga akai-akai, domin social media zai hadaka da sabbin mutane a koda yaushe da kayi login.

READ>>  [WhatsApp] Dalilan da Suke Saka WhatsApp Ke Dakatar da Mutum daga WhatsApp

4. Ka dinga tsara rubutu masu kyau da ya shafi abinda kake siyarwa ka sanya a blog ko website dink aka dinga yin sharing ta social media.

Reliable Web Hosting in Nigeria by DomainKing.NG

5. Ka dinga shiga duk tattaunawar da ta shafi bangaren abinda kake siyarwa wato dai ka shiga groups dake da alaka da abinda kake yi, tunda mu bama ban-bance group anan zance kayi kokarin shiga group me yawan jama’a tunda kowanne muna tallata hajarmu aciki.

6. Ka tsara kayanka a Social Media ta yadda zai saukakawa abokanan cinikayyarka domin maimakon sai sunzo shagonka a’a suna gida zasu ga kayayyakin ka sannan suyi order, kowan social media suna da tsarin tallansu wanda zaka iya amfani dasu.

7. Kayi amfani da HashTag wanda ya shafi abinda kake siyarwa domin zai taimaka maka wajen hadaka da masu neman irin kayanka da kuma wadanda kuke sana’a iri daya.

8. Ka dinga kawo batun tattaunawa wanda ya shafi kayanka wanda zai ja hankalin jama’a, hakan zai taimaka maka ka samu karin tunani iri-iri daga gun mutanen da bama kayi tsammani ba, sannan zai hadaka da masana wadanda suka fika ido ma a harkar wadanda baka san dasu ba, zaka iya haduwa da wadanda ke siyar da irin kayanka kuma akan farashi mai saukin da suma zaka iya siya a gurin su, baya ga masu siya a wurinka.

READ>>  [Cigaba] An Fara Dora Audio A Instagram

9. Ka tallata kayanka a social media kayi amfani da dukkan tsarukan talla da suke zuwa dashi, kamar Facebook promotion ko Instagram da sauransu wanda zaka biya su tallata maka kayanka.

10. Ka lura da like, comments da share da kake samu, domin daga sanda mutane suka fara yi maka like, comments da share to suna kara taimaka maka wajen tallan kayanka.

11. Ka dinga saurarar mabiyanka ta wajen amsa sakonninsu ta inbox, Mentioned da kuma bada amsa a comments, ta yadda zaka gamsar dasu.

12. Ka dinga sanya ra’ayoyin mutane game da kayanka, mabiyanka suna fadar ra’ayoyinsu akanka a posting dinka ko kuma suyi mentioned dinka, ko kuma bayan sun sayi kayanka suna godiya saboda ingancinsa to yana da kyau ka wallafa wannan bayanin (screenshot) domin kara jan hankalin sauran mabiyanka.

13. Ka dinga bincikar sababbin Customers yana da kyau ka dinga rarraba tallanka a groups da shafuka, sannan dole kayi hakuri da yanayin yadda mutane zasu zo maka.

14. Ka fahimci abokanan cinikinka, idan ka fahimci abokananka to sai ka maida hankali akan abinda zaka ja musu hankali kada ka sauka akan wannan.

READ>>  [Karanta Yanzu] Matsaloli Biyar (5) da Masu Kananan Sana’o’i ke Fuskanta

15. Idan mutane sukayi korafi akan wata matsala daga gareka to kayi kokarin maganceta da wuri.

16. Kadinga bibiyar labarai da rahotonni wanda ya shafi abinda kake siyarwa.

17. Ka san shin kayanka ma suwa kake son tallatawa? Misali inda kayan sawa na ‘yan shekara 18 to sune nake neman su sayi kayana, ko kuma a’a kayan mata ne zalla ko na maza.

18. Ka dinga tattara bayanan duk wadanda suka sayi kayanka ta social media.

19. Ka dinga kuma tattara adadin wadanda suka ga kayan naka koda kuwa basu siya ba, domin su san da kayan naka ma shima wata ribarce.

20. Ka dinga amfani da hoton da zai ja hankali wajen sanya tallanka a social media.

Allah ya bada sa’a.

Posted By: Basheer Sharfadi

E-mail info@hujjah.com.ng

About Author (117)

Administrator

Sunana: Sulaiman Aliyu Yahaya , Wanda Akafi Sani Da [Ibn Hujjah] Ni Haifaffen Garin Kano Ne, Nayi Karatuna Na Primary , A Nan Sheka Kumbotso L.G Nayi Secondry A G.S.S Shekar Barde, Nagama Karatuna Na Secondry, A Shekarar 2017, Yanzu Haka Ina Karatuna Akan Computer. Zaku Iya Kirana Ta No: 08163286393

2 responses to “[Online Business] Abubuwa Guda (20) Da Zasu Taimaka Maka Wajen Bunkasa Kasuwancinka Ta Social Media”

Leave a Reply
Our Android Application
Translate
Email Subscription
Saka email dinka kayi subsciption domin samun sabbin darussa a email dinka
Contact Us

Contact Us