<
Notice
Barka da zuwa Hujjah.Com.ng. Sanarwa, Wannan shafin An Gina Shine Domin Al'ummar Hausawa Gabadaya, Saboda Haka Kowa Ze Iya Regista Kuma Yayi Posting Acikin Shafin. Zaku iya tuntubar admin Contact Admin ko Facebook Page domin Aiko Mana Da Sakonninku, Mungode. info@hujjah.com.ng
HomeInternetHanyoyi 6 da zaka sanya mutane su dinga shiga Blog dinka

Posted by , June 10, 2019

Posted Under: Internet, 43 Views

Hanyoyi 6 da zaka sanya mutane su dinga shiga Blog dinka

A yau zanyi magana akan wasu hanyoyi guda 6 da zaka sanya mutane su dinga shiga blog dinka a koda yaushe.

1. Ka dinga wallafa bayanan masu amfani da shafinka, idan akayi maka comment na yabawa to kayi kokarin wallafashi domin wanda yayi zaiji dadi, sannan suma masu bibiyarka zasu kara samun gamsuwa da kai, sannan ka basu damar bayyana ra’ayoyinsu a comment.

2. Ka dinga yin reply ga masu aikowa da shafinka sakonni ta comment ko inbox.

3. Ka dinga yin sharing tsoffin postin misali yau nayi magana akanYadda ake satar account din facebookto akwai bukatar lokaci zuwa lokaci ka kara dawo dashi domin ka samu sabbin abokai an samu karin wanda basu karantashi ba a baya, wannan ga irin namu Bloggers din kenan ba masu Blog din Labarai ba.

READ>>  [Hosting] Menene Hosting, Dakuma Banbancin Free Hosting Da Paid Hosting

4. Ka dinga shirya zabe ko kacici-kacici/tambaya idan anci kayi yabo ko ka saka kyauta, wannan zai kara jawo maka hadin kan jama’a sosai, misali kwanaki shafinmu na Jaridar Tsanyaya sanya gasar cewa duk wanda ya fadi inda aka dauki wasu hotuna da ya wallafa za’a bashi 1,500 haka aka samu wata daliba ta amsa kuma aka bata kyautar, hakan ya janyowa shafin tarin jama’a sosai.

READ>>  [Online Payment] Yadda zaka tsara karbar kudi ta internet

5. Kada ka dinga wallafa rigingimu a shafunka, musamman rigingimun addini ko na kabilanci da makamantansu ka maida hankali kan iya abinda shafinka ya sanya gabam ka guji wallafa koda ra’ayinka na siyasa, misali a shafincomna internet da su Facebook bamu taba wallafa wani ra’ayinmu akai ba idan zamuyi wannan sai muyi amfani da personal account dinmu, haka akeso.

6. Ka baiwa masu ziyarar shafinka damar suyi subscribing ta email ta yadda kana wallafa abu zasu gani a email dinsu, sannan ka gayyacesu zuwa sauran shafukanka na social media.

READ>>  Yadda Zaka Gano Bayananka Da Kamfanin Google Da Facebook Ke Dauka Da Kuma Yadda Zaka Karesu

Allah ya taimaka.

Reliable Web Hosting in Nigeria by DomainKing.NG

About Author (117)

Administrator

Sunana: Sulaiman Aliyu Yahaya , Wanda Akafi Sani Da [Ibn Hujjah] Ni Haifaffen Garin Kano Ne, Nayi Karatuna Na Primary , A Nan Sheka Kumbotso L.G Nayi Secondry A G.S.S Shekar Barde, Nagama Karatuna Na Secondry, A Shekarar 2017, Yanzu Haka Ina Karatuna Akan Computer. Zaku Iya Kirana Ta No: 08163286393

1 responses to “Hanyoyi 6 da zaka sanya mutane su dinga shiga Blog dinka”

 • Thiѕ is a topic which is close to my һeart… Take care!
  Where arrе your contact detaiⅼs though?

 • Leave a Reply
  Our Android Application
  Translate
  Email Subscription
  Saka email dinka kayi subsciption domin samun sabbin darussa a email dinka
  Contact Us

  Contact Us