<
Notice
Barka da zuwa Hujjah.Com.ng. Sanarwa, Wannan shafin An Gina Shine Domin Al'ummar Hausawa Gabadaya, Saboda Haka Kowa Ze Iya Regista Kuma Yayi Posting Acikin Shafin. Zaku iya tuntubar admin Contact Admin ko Facebook Page domin Aiko Mana Da Sakonninku, Mungode. info@hujjah.com.ng
HomeFacebookHanyoyi (11) da Zaka Tsayar da Ganin Labaran Karya a – Facebook

Posted by , April 5, 2019

Posted Under: Facebook, 91 Views

Labaran Karya matsalace da ke ciwa da yawa daga masu amfani da shafukan facebook tuwo a kwarya,

domin kuwa abune da ya zamo ruwan dare ya kuma baza gari,

misali yanzu a facebookidan kayi searching din BBC Hausa, zaka samu akwai shafuka da dama kuma guda daya ne kacal mai inganci, don haka sai kaji mutum yace maka yaga labari a shafin BBC na facebook yayi ta rantsuwa karshe a binciko abin ba haka yake ba.

Yaduwar labaran karya kan iya haifar da tarzoma baya ga sanyawa mutane fargaba ta rashin tabbas, kai koda a musulunce ma karya haramunce.

Bara na tsahirta haka, Na koma kan jigon batun da nake magana,
zan kawo hanyoyin da mutum zai bi domin ya baiwa labaran karya takardar sallama daga Facebook dinsa.

PopAds.net - The Best Popunder Adnetwork

1. Ka nutsu sosai yayin da kaga wani labari, sannan ka duba waye ya saka labarin, kada ka gamsu don kaga link ko wani abu makamancin hakan, idan baka gamsu da labari ba kaje internet kayi searching ko ka tuntubi masana a bangaren.

READ>>  [Cigaba] Yadda Zaka Bude Account Din Banki Ta Facebook

2. Ka kula da shafuka masu alamar tantancewa Verified, duk shafin da kaga an bashi wannan alamar to shafine mai inganci.

3. Kayi reporting dinsa ta hanyar danna alamar report dake jikin kowane post.

4. Sannan kayi Unfollow ko Unfriend na duk wanda kaga ya saka labaran.

Reliable Web Hosting in Nigeria by DomainKing.NG

5. Kada kayi Like, Comment, ko React akan duk wani labari da baka gamsu da ingancinsa ba.

6. Ka cire duk wani abokinka da kaga yana yawan Like ko Comment akan labaran karya domin idan yayi kaima za’a nuna maka.

7. Ka tsara wadanda kake son ka fara gani a “News Feed” dinka,

Misali ka shiga manya shafuka ingantattu da mutane wanda ka tabbatar da ingancin abinda suke sakawa sai ka zabesu a matsayi na farko wato “See First”.

READ>>  [Facebook] Yadda Zaka Dawo Da Facebook Din Da Akayi Disable

Tsarin “See First” zai baka dama ka dinga ganin ingantattun sakonni,

Misali ni yanzu na saka manyan shafuka irinsu BBC Hausa, RFI Hausa, VOA Hausa, Daily Trust, Daily Nigerian, da sauran muhimman mutane dana gamsu dasu a matsayin “See First” wannan yasa idan na hau Facebook labaransu zan fara gani a News Feed dina to ina iya hawa Facebook har in sauka post dinsu kadai zan gani sai na ‘yan tsiraru don haka babu ni babu cin karo da labaran karya.

8. Ka lura da kyau daga taken labari, mafi yawan masu labaran karya kana iya ganeshi tun daga takensa.

9. Ka karanta sunan site a nutse domin tabbatar da ingancinsa misali com sai kaga wani site kuma bbchausanews.com idan kaga irin wannan to sai ka lura da asalin shafin mai inganci.

10. Bayan ka karanta labari ka kula da dalilin da suka kawo na hujjar tabbatar da labarin, idan babu hujja mai karfi to kada kayi saurin yarda dashi.

READ>>  [News] Zamu Shiga Kotu da Duk Masu Yin Cheat na Followers a Shafukanmu – Facebook

11. Labaran Wasa: Wasu labaran ban dariya ne ko kuma an kirkiresu ne domin nishadantarwa amman sai wani ya kallesu a matsayin labarai na gaskiya, to yana da kyau ka kula da wannan.

Nagode sosai da katsaya ka karanta wannan rubutun.

Posted by Basheer Sharfadi
Email: info@hujjah.com.ng

About Author (107)

Administrator

Sunana: Sulaiman Aliyu Yahaya , Wanda Akafi Sani Da [Ibn Hujjah] Ni Haifaffen Garin Kano Ne, Nayi Karatuna Na Primary , A Nan Sheka Kumbotso L.G Nayi Secondry A G.S.S Shekar Barde, Nagama Karatuna Na Secondry, A Shekarar 2017, Yanzu Haka Ina Karatuna Akan Computer. Zaku Iya Kirana Ta No: 08163286393

Leave a Reply
Email Subscription
Saka email dinka kayi subsciption domin samun sabbin darussa a email dinka
Contact Us

Contact Us