<
Notice
Barka da zuwa Hujjah.Com.ng. Sanarwa, Wannan shafin An Gina Shine Domin Al'ummar Hausawa Gabadaya, Saboda Haka Kowa Ze Iya Regista Kuma Yayi Posting Acikin Shafin. Zaku iya tuntubar admin Contact Admin ko Facebook Page domin Aiko Mana Da Sakonninku, Mungode. info@hujjah.com.ng
HomeInternet[Blog SEO] Abubuwa 10 da zaka bunkasa SEO a Blog dinka

Posted by , June 11, 2019

Posted Under: Internet, 56 Views

[Blog SEO] Abubuwa 10 da zaka bunkasa SEO a Blog dinka

Da yawan Bloggers dinmu na AREWA suna jin jiki saboda matsalar SEO wasu saboda rashin sani, wasu kuma saboda rashin bin doka da ka’ida, tabbas SEO yana daga cikin manyan matsalolin da AREWA Bloggers ke fuskanta, domin duk site din da SEO dinsa baya motsawa to tabbas sunansa gawa, domin samun Traffic ta Google shine mafi albarka da alkhairi fiye da samu ta Facebook dasu WhatsApp.

A yau nayi nazari kan wasu hanyoyi guda goma (10) da Blogger zaibi domin bunkasa SEO a Blog dinsa.

1. Kayi amfani da kalmomin da mutane ke bincika (keyword search) misali mutane suna yawan shiga internet su rubuta yadda ake abu kaza, to idan kazo yin post sai kayi amfani da yadda ake abu kaza, to da zarar mutane sun binciki wannan abun zai hanzarta kawo musu site dinka.

2. Ka saka keyword sama da guda daya a wurin tagging, misali nayi rubutu akan Yadda ake bude email to a wurin tag zan iya saka Yadda zaka bude email, Yaya zan bude email, ina son bude email, yadda duk wanda akayi searching zai wurga masa amsarka, a kowane post akwai wurin taggin.

READ>>  [Online Money] Hanyoyi Goma Sha Takwas [18] da Zaka Iya Samun Kudi ta Internet

3. Ka saka take rubutu mai jan hankali, yana da kyau ka kula da kyau wajen saka taken da zai ja hankali misali zanyi rubutu akan blogging sai na saka Ma’anar Blogging da Abinda ya kunsa, ko kuma Yaya ake yin abu kaza da sauran Title wanda kana ganin mutum zai iya bincikar wannan taken.

4. Ka dinga saka Back Link a duk sanda kayi magana akan wani abu to kayi mention dinsa, kamar yadda kuke gani a wannan shafin duk sanda wani bayani ya biyo ta kan wani ko wata gaba da mun riga munyi bayani akanta to mukan yi mentioned dinta ta yadda zaku ga gun yayi highlighting kawai dannawa zakuyi, hakan yana taimakawa SEO sosai da sosai.

1. Sanya hoto a posting yana da kyau idan zakayi posting kayi amfani da hoto kuma ka sanyawa hoton sunan post din da kayi misali nayi posting akan yadda ake samun kudi da facebook to sai na sakawa hoton suna “how to make money with facebook”.

READ>>  Yadda Zaka Gano Bayananka Da Kamfanin Google Da Facebook Ke Dauka Da Kuma Yadda Zaka Karesu

2. Ka sanya ALT Text a hoton da ka saka, idan kazo dauko hoto akwai wurin Alt Text ana bukatar nan ma ka saka bayanin abinda hoton ya kunsa sau tari shima muna saka abinda mukasa a tag a wajen hakan zai sanya da anyi searching a internet ya bayar da hoton.

Reliable Web Hosting in Nigeria by DomainKing.NG

3. Ka sanya Image Description idan kazo dauko hoto akwai wurin Description da zaka rubuta takaitaccen bayani akan abinda hoton ya kunsa, shima wannan yana matukar taimakawa SEO dinka.

4. Ka saukaka bayaninka, kada kazo kayi bayani mai tsauri ko wanda ba zai gamsar da al’umma ba domin hakan ka iya hana al’umma shiga shafinka, kaga kai kuma ba haka kakeso ba.

5. Ka tabbatar ka zabi Category a posting dinka misali kayi posting akan Facebook ko labarai to ya zama kana da folder ta facebook ko labarai da zaka sanya wannan post din.

READ>>  [Hosting] Menene Hosting, Dakuma Banbancin Free Hosting Da Paid Hosting

6. Ka dinga saka “Related Post” kada ka damu da wanda site dinka ke sakawa Automatically, a’a ka sanyashi da kanka wani a tsakiya wani a kasa kamar misali a wannan post din kunga a sama mun baku wani link related da mukace Karanta wannan sannan a kasa zamu kara baku Rubutuka Masu Alaka: ku dinga yin wannan domin site zai iya kawo post din da basu sukafi can-canta suzo a related ba.

Posted By: Basheer Sharfadi.
Email: info@hujjah.com.ng

About Author (117)

Administrator

Sunana: Sulaiman Aliyu Yahaya , Wanda Akafi Sani Da [Ibn Hujjah] Ni Haifaffen Garin Kano Ne, Nayi Karatuna Na Primary , A Nan Sheka Kumbotso L.G Nayi Secondry A G.S.S Shekar Barde, Nagama Karatuna Na Secondry, A Shekarar 2017, Yanzu Haka Ina Karatuna Akan Computer. Zaku Iya Kirana Ta No: 08163286393

1 responses to “[Blog SEO] Abubuwa 10 da zaka bunkasa SEO a Blog dinka”

 • I enjoy reading through a post that can make men and women think.
  Also, thank you for permitting me to comment!

 • Leave a Reply
  Our Android Application
  Translate
  Email Subscription
  Saka email dinka kayi subsciption domin samun sabbin darussa a email dinka
  Contact Us

  Contact Us